HUKUNCIN AMFANI DA MAGANIN INHELA GA MAI AZUMI
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Menene hukuncin amfani da maganin fesa iska a cikin bakin mai azumi da rana (wato, inhela), saboda ciwon quncin qirji ko wahalar numfashi (Asma)?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
Hukuncinsa shi ne halacci; idan har lalura ta buqatar da mutum zuwa ga hakan, saboda fadin Allah Mabuwayi da daukaka a cikin "suratul An'aam ayata 119":
وَقَدْ فَصَّلَ لَكُم مَّا حَرَّمَ عَلَيْكُمْ إِلَّا مَا اضْطُرِرْتُمْ إِلَيْهِ
Ma'ana: "Kuma ya muku bayani na dalla-dallan abinda ya haramta akanku, sai dai wanda lalura ta buqatar da ku zuwa gare shi"
:
Kuma saboda kasancewar inhela baya kamantacceniya da ci ko sha, sai ya yi kama da jinin mutum da ake dauka don aunawa ko bincike, ko kamar allurar da ba a sanya abinci a cikinta ba.
:
Duba cikin littafin: TUHFATUL IKHWAN BI AJWIBATIN MUHIMMATI TATA'ALLAQU BI ARKAANIL ISLAAM.
:
MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 265).
Allah ta'ala yasa mudace.
:
Related Posts
Trending Discussions
Are you ready!!!
How prepared are you to get married? What is the one thing that is stopping you?
General
Why is it that working class guys like me only meet idle ladies
I find it hard to understand why ladies that don't work or do business or have money wants to get ma...
Read more
Relationship
TEAM LEFE DOLE KO ASOKE LEFE
A ra'ayin ki/ka a soke lefe ko a'a. Ni nawa ra'ayin yafi ga a soke kawai.
Marriage
A Message to My Princess (unknown wife)
Assalamu alaikum!
how are you doing my princess? first I would like to say I'm so sorry it's been 8...
Read more
Marriage
Me yake fara zuwan ranka idan kayi tunanin Aure?
Aduk Lokacin Da Kayi Tunanin Yin Aure Me Yake Fara Zuwa Ranka?
Marriage
Join the Discussion
Sign in to share your thoughts and engage with the community.
Login to Comment